News
Mutum 25 Sun Mutu A Yayin Da Sabuwar Mugunyar Cuta Ta Bulla A Kano.
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
A kalla mutane 15 ne suka rasu sakamakon abin da ake zargi cutar diptheria ne a jihar Kano zuwa ranar 18 ga watan Janairu, a cewar Dr Abdullahi Kauran-Mata, masanin cututtuka masu yaduwa.
Ya ce an samu mutum 78 masu dauke da cutar mai gaggawar yaduwa a kananan hukumomi 14 na jihar.
Kauran-Mata ya fada wa kamfanin dillancin labarai NAN, a ranar Alhamis a Abuja, cewa an dauki samfuri guda 27 an kai su dakin gwaji, an tabbatar da takwas kuma mutane uku sun mutu a jihar.
Ya ce: “A halin yanzu gwamnatin jiha ta kafa cibiyar kula da masu diphtheria da tallafi daga kungiyoyin tallafawa al’umma na Médecins Sans Frontières (MSF) a asibitin kwararru na Murtala Muhammad inda ake kula da masu dauke da cutar.
“An kuma fara sanarwa a gidajen radio tare da tattaunawa kan cutar. “Gwamnatin jihar ta kuma kafa tawaga mai kula da yaduwar cutar karkashin jagorancin jami’in kula da bullar annoba don saka ido.”
Kauran-mata ya ce ana iya kare kamuwa da diptheria ta hanyar rigakafi.
A cewarsa: “Amma, kananan yara ake yi wa rigakafin karkashin tsarin riga kafi na kasa.
Sauran hanyoyin kare kai daga kamuwa sun hada da saka takunkumin fuska, wanke hannu da tsafta, takaita taba wadanda suka kamu da kai su asibiti cikin gaggawa.”
