Connect with us

News

Mutum miliyan 2 ne suka rasa muhallansu a Najeriya saboda ambaliyar ruwa- NEMA

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

 

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) Mustapha Ahmed ya ce mutum miliyan 2.4 ne suka rasa muhallansu sakamakon matsalar ambaliyar ruwa da ta shafi wurare daban-daban a daminar 2022.

Advertisement

 

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja lokacin buɗe taron mako guda ma masu ruwa da tsaki na hukumar suka shirya.

Advertisement

Za mu haɗa hannu da EFCC domin hana sayen ƙuri’a a zaɓen bana – INEC

Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ruwaito cewa mahalarta taron sun haɗar da shugabanni hukumar na rassan jihohin ƙasar, da sauran hukumomin da ke taimak wa hukumar.

 

Advertisement

Mista Ahmed ya ce taron wanda zai horar da jami’an hukumar game da ayyukansu – an shirya shi ne a daidai lokacin da ƙasar ke farfaɗowa daga ɓarnar da ambaliyar ruwar ta haddasa.

 

Advertisement

”Bayanai sun nuna cewa mutum 662 ne suka rasa rayukansu, wasu kimanin 3,174 suka samu raunuka, sai kuma miliyan 2, 430, 445 da suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar”, in ji Mista Ahmed.

 

Advertisement

Ya ƙara da cewa dubban gidaje ne suka rushe yayinda gonaki masu yawa da kadarori suka gurɓace sakamakon bala’in.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending