News
Ambaliyar ruwa ta shafi ‘yan Najeriya sama da miliyan 4 a 2022 – NEMA
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta shafi ‘yan Najeriya sama da miliyan hudu a shekarar 2022.
Da yake jawabi a ranar Alhamis a garin Uyo yayin kaddamar da shirin matakan gargadin tunkarar bala’i ga al’ummar ƙasar, babban daraktan hukumar NEMA, Ahmed Mustapha Habib ya ce a shekarar 2022, sama da mutane miliyan 4 ne ambaliyar ta shafa a Najeriya.
INEC Ta Bayyana Ranar Da Za Ta Fara Duba Sakamakon Babban Zaben 2023
Ya ƙara da cewa, ambaliyar ta yi sanadin mutuwar ‘yan Najeriya 665, sama da mutane miliyan 2 kuma sun rasa matsugunnai, baya ga cinye gidaje 355,986, ta kuma mamaye kadada 944,989 na gonaki.
Shugaban ya bayyana cewa, domin duba yadda ambaliyar ruwa ta auku, hukumar tare da hukumar kula da yanayi (NiMet), da hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya (NIHSA) sun tura ƙwararru zuwa jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Matakin in ji shi zai taimaka wajen tabbatar da tsarin samun gargadin zuwan ambaliyar ruwa cikin gaggawa kafin damuna ta gama kamawa.
BBC Hausa
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
