Connect with us

News

INEC Ta Bayyana Ranar Da Za Ta Fara Duba Sakamakon Babban Zaben 2023

Published

on

INEC Logo

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ce za ta fara duba sakamakon babban zaben shekarar 2023 wanda za a yi a watan Yuli mai zuwa kamar yanda jaridar Daily Post ta rawaito.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe.

Advertisement

An fara cire tsammaninn ceto attajiran da suka nutse a teku

Sanarwar ta fito ne bayan taron da INEC ta yi na yau Alhamis a Abuja.

Okoye ya bayyana cewa matakin ya dace da tsarin da Hukumar ta yi na tsawon shekaru.

Advertisement

A cewarsa, bitar za ta mayar da hankali ne kan dukkan harkokin zabe kafin zabe da lokacin da kuma bayan zaben.

Okoye ya ce bitar za ta hada da jami’an hukumar a matakin kasa da jihohi da masu ruwa da tsaki da nufin koyar da darasi da kuma tsara hanyoyin da za a bi.

Advertisement

“Za a fara yin bitar ne da taron da RECs za ta yi a ranar 4 ga watan Yuli kuma za ta kare da janyewar hukumar a ranar 5 ga watan Agusta,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending