News
Hisbah Ta Fara Binciken Matar Da Ta Auri Saurayin Ƴarta A Kano
DAGA KHADIJA NASEER MUSA
Babban kwamandan hukumar Hisbah Sheikh Harun Ibn Sina ya ce ya kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike game da zargin da ake yi wa wata mata a jihar na kashe aurenta tare da auren saurayin ƴarta.
Iyayen matar ne dai suka yi ƙorafin cewar shugaban Hisbah na ƙaramar hukumar Rano ya aurar da ƴar tasu ba tare da izininsu ba.
An saki magoya bayan Arsenal da aka kama kan wasansu da Manchester United
“Kwanaki biyu da suka gabata ne labari ya iso teburina cewa wata mata ta kashe aurenta, inda kuma ta auri saurayin ƴarta, saboda haka nan take na kafa kwamiti domin yin bincike game da batun”.
“Mun gayyato duka ɓangarorin da lamarin ya shafa”.
“Kuma da zarar kwamitin ya kammala bincike za mu sanar wa duniya halin da ake ciki”
Babban kwamanda Hisbah na Kano ya kuma ce wannan labari ne mai rikirtawa da ba su taɓa ganin irin sa ba.
”Duk da cewa muna samun matsaloli masu yawa a kowace rana, to amma a tsawon lokacin da na kwashe a matsayin kwamandan hukumar, wannan shi ne karo na farko da na samu labari makamncin wannan, hakan bai taɓa faruwa ba”, in ji Ibn Sina.
Yadda lamarin ya faru
Kawun matar, mai suna Abdullahi Musa Rano ne ya fara gabatar da ƙorafin ranar Litinin da daddare a gidan Radiyon Freedom da ke jihar Kano, inda ya zargi shugaban Hisba na ƙaramar hukumar Rano da aurar da ƴarsu ga saurayin ƴarta, bayan ta kashe aurenta da mijinta.
Abdullahi ya ce abin da ya faru abin kunya ne ga danginsu, kuma abu ne da ba za su bari ya kasance ba.
“Ta takura wa mijinta har sai da ya sake ta, domin ta auri wannan mutumin. wannan abin kunya ne ga danginmu, domin haka muke kira ga kwamandan hukumar Hisbah da gwamnatin jihar Kano da su duba wannan batu”.
Wani mazaunin ƙaramar hukumar Rano mai suna Sabiu Sani wanda kuma ya san labarin ya shaida wa BBC cewa tabbas yarinyar ta ƙi amincewa da soyayyar saurayin nata duk kuwa da ƙoƙarin da ya yi na jan hankalinta.
“Matar na ganin cewa a maimakon ita da ƴar tata su yi biyu babu a kan mutumin da take ganin cewa mutumin kirki ne, shi ya sa ta ga cewar ya kamata ita ta aure shi, tun da ita ƴar tata ba ta son sa”.
“Abin da ya faru abu ne mai rikitarwa don haka ne mutane ke ta maganar a ko’ina a cikin garinmu a daidai wannan lokaci.”
Sabi’u ya ce a yanzu ba su san inda ma’auratan suke ba.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
