Connect with us

News

Ahmed Usman-Ododo Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar Kogi A Jam’iyyar APC

Published

on

A wani labarin kuwa, zaben fidda gwani na gwamna a jihar Kogi karkashin jam’iyyar APC da aka gudanar a jiya ya dauki wani sabon salo, yayin da mataimakin gwamnan jihar , Edward Onoja, ya janyewa babban bincike kudi na jihar, Ahmed Usman-Ododo takarar.

 

Wasu ’yan takara bakwai da suka hada da tsohon Kwamishinan Kudi, Mista David Adebanji-Jimoh da Asiwaju Ashiru Idris da Okala Yakubu, suma suma sun janyewa Usman-Ododo takarar biyo bayan amincewa da takararsa da Gwamna Yahaya Bello ya yi.

Yan Najeriya Sama Da Milyan 1 Ne Suka Ci Gajiyar Shirin Rage Fatara A Nigeriya

Sauran sun hada da Abdulkareem Asuku wanda shine shugaban ma’aikata na gwamna yahaya Bello da kuma Babban Akantan jihar Momoh Jibrin.

 

Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jihar, Wanda kuma shine gwamnan jihar Zamfara, Gwamna Mohammed Bello-Matawale shine ya tabbatar da faruwar lamarin bayan zaben fidda gwanin da aka gudanar a jiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending