News
Zaɓen Ghana: Jam’iyyar NDC ta zaɓi Mahama a matsayin ɗan takararta
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An zaɓi tsohon shugaban ƙasar Ghana John Mahama a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawa ta NDC a babban zaɓen ƙasar da ke tafe cikin shekara mai zuwa.
A ranar Lahadi ne aka ayyana John Mahama a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar ta gudanar, inda ya samu kashi 98.9 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen da aka gudanar jiya Asabar
John Mahamaya samu nasara ne a kan abokin takararsa tsohon magajin garin Kumasi Kojo Bonsu.
Shi kuwa ɗan takara na uku a zaɓen Dakta Kwabena Dufour janyewa ya yi daga takarar bayan da ya yi zargin aikata ba daidai ba atsarin gudanar da zaɓen.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita bayan samun nasara, Mista Mahama ya yi kiran samun haɗin kai a jam’iyyar.
Wannan shi ne karo na uku da Mista Mahama ke takara, a yunƙurin da yake yi na komawa kan mulki, tun bayan shan kaye da ya yi a shekarar 2016 a hannun shugaban ƙasar na yanzu Nana Akufo Addo, wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu a shekara mai zuwa.
John Mahama ɗan siyasa ne da ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaban ƙasa, sannan ya zama shugaban ƙasa bayan rasuwar shugaban ƙasar na wancan lokaci John Evans Atta Mills.
Ya tsaya takara a zaɓen 2012, inda ya yi nasara, sai dai wa’adi ɗaya kawai ya yi, kafin ya sha kaye a zaɓe 2016.
