Connect with us

News

Lalata Asibitoci A Fadan Sudan Ya Jefa Majinyata Mawuyacin Hali

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Yakin da ake gwabzawa a Sudan ya lalata asibitoci da kuma cibiyoyin kula da lafiya a kasar, kuma majinyatan da suka tsere daga rikicin na neman magani.

muryar amirika ta rawaito cewa Yayin da ake fama da rashin tallafin jinya, wani mai harhada magunguna dan kasar Sudan da ya tsere daga Sudan a makonnin da suka gabata yana yin duk mai yiwuwa don taimakawa wasu ‘yan gudun hijira a wani sansani a makwabciyar kasar Chadi.

Advertisement

 Babu wani yankin Najeriya da ke hannun ‘yan ta’adda – Monguno

A watan daya da ya gabata, Mohammed Adam ya tattara irin magungunan da zai iya a lokacin da ya ji kungiyar Janjaweed, wata kungiyar da ta shahara wajen kashe fararen hula, na shirin kai hari garinsu na Tendelti a yammacin Darfur. Ya ce ya loda magungunan ne a kan keken doki, inda ya yi tafiya mai nisan kilomita ko makamancin haka ya tsallaka kan iyaka zuwa makwabciyar kasar Chadi.

Tun daga wannan lokacin, ya kafa wani kantin magani na wucin gadi a Koufroune, wurin ‘yan gudun hijira inda kusan mutane 10,000 ke zaune.

Advertisement

Tun lokacin da rikicin Sudan ya fara a ranar 15 ga Afrilu, Chadi da kungiyoyin agaji sun yi ta kokawa wajen samar da isasshen abincin da ‘yan gudun hijira za su ci. Agajin magani yana da karanci, a cewar ‘yan gudun hijirar.

A cikin Sudan, tsarin kula da lafiya ya durkushe.

Advertisement

Wani faifan bidiyo na ya nuna wani asibiti a birnin Khartoum da fada ya kone kurmus. Wasu kuma a birnin an ce sun samu mummunar barna, tare da asibitoci a yammacin Darfur, inda ake gwabza kazamin fada.

Kungiyar likitoci masu zaman kansu ta Doctors Without Borders ta fada ranar Talata cewa an wawashe kayan aikinta, yayin da aka kashe ma’aikaci a cikin watan Afrilu a fadan. Ta ce kwasar ganima za ta haifar da sakamako na “rashin rai” ga al’ummar Sudan.

Advertisement

Ameir Eltom shine mataimakin sakatare-janar na kungiyar Likitocin Amurka ta Sudan. Ya ce kasancewar gwamnatin Sudan ba ta aiki saboda fadace-fadacen da ake yi, kungiyarsa na taimakawa wajen gudanar da ayyukan wasu asibitoci.

Tsagaita wuta na mako guda da aka fara ranar litinin ya kamata ya ba da damar wasu kayan agajin jinya shiga kasar.

Advertisement

Ya roki duk kungyoyi masu zaman kansu da kuma al’ummomin gida da su taimaka wa ‘yan gudun hijirar saboda da gaske suna bukata. Ba su da wurin da za su kare kansu daga ruwan sama, wanda ke taimakawa wajen yada cututtuka. Ya kuma damu da yaduwar cutar kwalara, wacce za ta iya rikidewa zuwa annoba, wadda za ta zama bala’i.

Ya ce yana yin abin da zai iya, da dan abin da yake da shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending