Connect with us

News

Amirka ta sanya takunkumi ga jagoran Wagner a Mali

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

kasar Amirka ta ce jagoran,  Ivan Maslov babban jigo ne a harkokin kamfanin Wagner a duniya. Amirkar dai ta zargin kamfanin Wagner da ke aiki a Mali da wasu kasashen Afirka da yunkurin tattara makamai da jirage marasa matuka da kayayyakin yaki domin ci gaba da yakar Ukraine.

Sai dai har kawo yanzu gwamnatin Malin bata mayar da martani kan wannan zargin ba. A share guda Amirka ta zargi kamfanin da bai wa dakarun RSF a Sudan na’urorin kakkabo makamai masu linzami da ta ce ka iya kara musu karfin iko wajen yakar dakarun sojin Sudan.

Advertisement

Babu wani yankin Najeriya da ke hannun ‘yan ta’adda – Monguno

Kasashen Yamamcin Turai dai na nuna damuwarsu kan ayyukan kamfanin Wagner a Mali tun a shekarar 2021, inda kamfanin ke taimakawa Mali a yakin da gwamnati ke da ‘yan ta’adda.

 

Advertisement

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending