Connect with us

News

Babu wani yankin Najeriya da ke hannun ‘yan ta’adda – Monguno

Published

on

DAGA  MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN

Gwamnatin Najeriya tace babu wani yankin kasarta dake karkashin ‘yan ta’addan book haram ko ISWAP kamar yadda wasu jama’a ke ci gaba da hasashe a cikin kasar.

Advertisement

Mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Janar Babagana Monguno ya bayyana haka, bayan wani taro na musamman da majalisar zartarwar kasar ta gudanar wanda shine irinsa na karshe kafin mika mulki ga sabuwar gwamnati.

Ƴan sandan Ghana sun kama ƴan Najeriya 49 kan zargin safarar mutane

Janar Monguno yace lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi ragamar mulkin Najeriya a shekarar 2015, kananan hukumomi 17 ke karkashin ikon kungiyar boko haram, amma kuma sakamakon kara kaimin da sojoji suka yi da kuma samun makamai na zamani, an kubutar da wadannan yankuna daga mamayar da aka musu a jihar Borno.

Advertisement

Mai baiwa shugaban kasar shawara yace gwamnatin Buhari ta samu gagarumar nasara wajen yaki da ‘yan ta’adda da kuma tabbatar da zaman lafiya a sassa daban daban na kasar.

Janar Monguno ya kare matakin da gwamnati ta dauka na takaita safarar takin zamani saboda yadda ‘yan ta’adda ke amfani da shi wajen sarrafa bama bamai, wadanda suka dinga tashi a sassan Najeriya tun kafin fara mulkin Buhari, yayin da yace sun samu nasara yanzu tashin bama baman ya zama tarihi.

Advertisement

Mai baiwa shugaban kasar shawara yace yanzu abinda ake gani, shine yadda ‘yan ta’addan ke kai hari suna guduwa irin na sari-ka-noke, sabanin yadda suka mamaye yankuna a baya.

Janar Monguno ya kuma bukaci ci gaba da taka rawar malaman addini wajen sauya tunanin irin wadannan mutane da kuma koyar da ilimin addini kamafr yadda aka saba, sabani gurguwar akidar da ta haifar da matsalar book haram a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending