Connect with us

News

Rundunar Yan Sanda Sun Gano Wasu Shanu Da Suka Bace A Kano.

Published

on

Shanu

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta gano wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba da ke yawo a unguwar Ranka Hotoro da ke karamar hukumar Tarauni a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar sandan jahar kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya rabawa manema labarai a Kano ranar Lahadin nan.

Yau kwanaki 40 kenan da tsohon shugaban Hukumar EFCC, ke tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS.

Kiyawa ya ce, wani mutumin kirki ne ya ga shanun da suka bace a ranar 13 ga watan Yuli kuma ya ja hankalin ofishin rundunar ‘yan sanda na Hotoro.

mutum  ya shaida wa ’yan sanda cewa a kan hanyarsa ta zuwa Rakat Hotoro Quarters Kano, ya ga wasu shanu suna yawo sama da sa’o’i uku.

Advertisement

“Bayan samun rahoton, an tuntubi mazauna yankin kuma an kokarin gano masu shanun wanda hakan ya ci tura,” in ji shi.

Hakazalika sanarwar ta ce a ranar 14 ga Yulin 2023, wani mutum ya ba da rahoton ganin wata jaka wadda ake kyautata zaton ta fasinja ce da ya dauko a cikin baburin adaidaita sahu.

An kai rahotan ne ofishin ‘yan sanda na Hotoro kuma duk kokarin da aka yi na gano mai ita lamarin ya ci tura,” in ji shi.

Jaridar DailyNigerian ta rawaito cewa Sanarwar ta shawarci mazauna garin Kano da ke neman neman dukiyoyin da suka bata da su ziyarci ofishin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, a shedikwatar ‘yan sandan Kano, tare da shaidar mallakarsu.

NAN

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending