News
Rundunar ‘Yan sandan Jigawa sun kama barayin shanu Tare da kwato shanu uku
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi barayin shanu, Umar Musa da Idris Ismail, tare da kwato shanu uku da kudinsu ya kai N1.15m.
Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Talata.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ranar 13/11/2023 da misalin karfe 08:00, wani Umar Musa dan shekara 20 da Idris Ismail mai shekaru 30 da haihuwa duk a kauyen Malamawa, karamar hukumar Kiyawa, sun shigar da kara kai tsaye hedikwatar ‘yan sanda ta Kiyawa cewa, A ranar da misalin karfe 03:00 na safe wasu barayi da ba a san ko su waye ba suka hada baki tare da kutsawa cikin gidajensu tare da sace shanu uku da kudinsu ya kai N1.15m.
“Bayan samun rahoton, jami’an bincike daga sashin Kiyawa sun yi cikakken bayani.
“Bayan bayanan da aka samu, an gano shanun guda uku da aka sace an kuma gano su a gidan wani Muktari Ibrahim ‘m’ mai shekaru 23 a Sabuwar Unguwa, karamar hukumar Kiyawa.
“A lokacin da aka tambaye shi, Muktari ya bayyana cewa ya karbi shanun ne daga hannun wani Yusuf wanda a halin yanzu yake tsare.”
