News
Dakarun sojin jamhuriyar Nijar sun kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wadansu sojoji kalilan ne suka sanar da yin juyin mulkin ta gidan Talabijin na kasar a daren jiya, Yan sa’oi bayan da sojojin suka yiwa shugaban kasar daurin tala-la a gidansa dake fadar shugaban kasa.
Kazalika sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin kasar da kuma dukkanin wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati, tare da kulle iyakokokin shige da fice na kasar, inda suka baiyana cewar sunyi juyin mulkin ne saboda halin tabarbarewar shugabanci da kasar ta tsinci kanta a ciki.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Ya Sauka Daga Kan Kujerarsa
Da yake karanta sanarwar yin juyin mulkin, Kanal Amadou Abdramane, wanda wasu sojoji guda tara suke zagaye da shi, Ya ce sojoji sun kwace mulkin jamhuriyar Nijar.
Advertisements
