News
Yau Za A Buɗe Kantin Shoprite A Kaduna – Uba Sani
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kaduna da ake Arewacin Najeriya, Malam Uba Sani ya sanar da al’ummar cewa a yau Alhamis za a bude babban kantin nan na sayar da kayayyaki wato Shoprite.
Malam Uba Sani ya sanar da haka ne a yau Alhamis a shafinsa na Facebook, kuma ya ƙara da cewa akwai rangwame na musamman ga mutanen da za su sayi kaya a shagon na Shoprite a lokacin bikin buɗewar.
Dakarun sojin jamhuriyar Nijar sun kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum.
Matasa da dama kan yi wa kantin Shoprite tsinke da ke jihar Kano a lokutan bukukuwa inda suke yin sayayya sannan su dauki hotuna.
Advertisements
