News
Jamhuriyar Nijar za ta kyale Burkina Faso da Mali su shiga kasarta don taya ta fada
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sojojin da suka kwace mulki a Jamhuriyar Nijar a watan jiya sun ce za su bai wa dakarun kasashen Burkina Faso da Mali izinin shiga kasar “idan har aka takale mu da yaki.”
Ministocin harkokin wajen Burkina Faso da Mali, Olivia Rouamba da Abdoulaye Diop, sun ziyarci birnin Niamey a ranar Alhamis, inda shugaban gwamnatin juyin mulki ta Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya karbi bakuncinsu.
Sun yi maraba da sanya hannu kan izinin bai wa sojojin Burkina Faso da Mali umarnin “shiga cikin Nijar idan har aka takale mu da yaki,” a cewar sanarwar da mataimakin sakatare janar na harkokin wajen Nijar ya karanta.
Sojojin ne suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin, lamarin da ya jawo kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS yin barazanar amfani da karfi don mayar da shi.
Nijar ce kasa ta hudu da aka yi juyin mulki a Afirka ta Yamma tun daga shekarar 2020, bayan Burkina Faso da Guinea da Mali.
Sojojin juyin mulkin Burkina Faso da Mali sun ce idan dai aka yi amfani da karfin soja a makwabciyarsu to hakan “tamkar buga gangar yaki ne” kan kasashensu.
Sannan Janar Tchiani ya yi gargadi a wani jawabi da ya yi da aka watsa a talabijin ranar Asabar cewa, “idan aka kawo mana hari, to lamarin fa ba zai kasance kamar yadda mutane ke tunani ba.”
A farkon wannan watan ne, ECOWAS ta ce mamobinta 11 cikin 15 sun amince a yi amfani da karfin soji idan hanyar diflomasiyya ta ci tura.
Ana ganin Nijar a matsayin daya daga cikin kasashe na karshe da ke bin tsarin dimokuradiyya a yankin Sahel da ke kusa da Hamadar Sahara, wacce kasashen Yammacin Duniya za su yi amfani da ita wajen yaki da masu tsattsauran ra’ayin addini da ke kara yaduwa na kungiyoyin da ke da alaka da Al Qaeda.
Faransa da wasu kasashen Turai da Amurka sun kashe makudan miliyoyin daloli wajen samar da kayan yaki da horar da sojojn Nijar, ita kuwa Faransa har ayyukan hadin gwiwa na soji suke yi tare.
Zaben Bazoum da aka yi a shekarar 2021 wata gagarumar nasara ce da ta bude wa kasar hanyar mika mulki daga gwamnatin farar-hula zuwa wata gwamnatin farar-hular cikin lumana.
Sau biyu Bazoum yana tsallake kokarin yi masa juyin mulki kafin daga karshe a yi nasarar hambarar da shi, a juyin mulki na biyar da ya faru a kasar tun bayan samun ‘yancin kanta daga Faransa
a shekarar 1960.
TRT