News
Hannatu Musa Musawa: An Bankado Wani Sabon Laifin Ministar Tinubu
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
An sake taso sabuwar ministar fasaha, al’adu da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musa Musawa, a gaba Ana zarginta da saɓawa tanadin kundin tsarin mulki wanda hakan ya sanya zamanta minista ya saɓa doka
A cewar ƙungiyar HURIWA, Hannatu yanzu haka tana yin bautar ƙasar ta (NYSC) a birnin tarayya Abuja.
Jamhuriyar Nijar za ta kyale Burkina Faso da Mali su shiga kasarta don taya ta fada
Ana zargin Hannatu Musa Musawa, ministar fasaha, al’adu da tattalin arziƙin fikira, da kasancewa mai yin bautar ƙasa (NYSC) ƙafin naɗin da Shugaba Tinubu ya yi mata.
Kamar yadda Arise TV ta rahoto, ƙungiyar HURIWA ita ce ta yi zargin, inda ta nuna cewa naɗin da aka yi mata ya saɓa doka
Ƙungiyar ta yi zargin cewa ministar tana bautar ƙasa ne a jihar Ebonyi, amma ta tsallake ta daina domin zama minista wanda a doka ba ta cancanta ba.
An tattaro cewa tun a shekarun baya aka tura ta yin bautar ƙasar amma sai ta fasa, sannan daga baya ta dawo ta nuna sha’awar tana son kammalawa.
Ƙungiyar ta bayyana cewa: “Sashe na 13 na dokar NYSC, ya gindaya cewa duk wani ɗan Najeriya da ya kammala karatun digiri ko HND mai ƙasa da shekara 30 wanda ya ƙi zuwa yin bautar ƙasa na shekara ɗaya, ya aikata laifi wanda ya cancanci hukuncin tarar N4,000 ko ɗaurin shekara biyu a gidan kaso, ko hukuncin tara da zaman gidan kaso.”
Ƙungiyar ta tabbatar da cewa majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa har yanzu ministar ƴar bautar ƙasa ce kuma ba ta kammala ba. Bayanan ɓautar ƙasar ta sun nuna lambar NYSC ɗinta a matsayin FC/23A/505 sannan an tura ta ne zuwa kamfanin Onyilokwu Onyilowa a ‘Paint house old Banex