News
Jami’ar Bayero Za Ta Hada Aurataiya Tsakanin Ma’aikatanta
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’I ta kasa, SSANU, reshen Jami’ar Bayero, ta shirya bullo da wani tsari na yin auratayya a tsakanin ‘ya’yan kungiyar ta SSANU.
Jami’ar kungiyar bangaren Mata, Farida Sani Kamba ce ta bayyana haka a ranar Alhamis a nan Kano yayin taron kaddamar da taron matan kungiyar manyan ma’aikatan jami’ar bayero.
Hannatu Musa Musawa: An Bankado Wani Sabon Laifin Ministar Tinubu
A cewarta, shirin na da nufin inganta zamantakewar aure a tsakanin yan kungiyar
Ta ce hada auratayya a tsakaninsu zai temaka wajen saukaka ayyukansu yadda ya kamata , Kasancewar kowannensu ya fahimci yadda tsarin aikinsu ke kasancewa.
Advertisements
