News
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf Zai Samar Da Sana’oin Dogaro Da kai Ga Tubabbun Masu Aikata Lefi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf Ya yi alkawarin samarwa matasan da suka tuba daga aikata lefuka sana’oin dogaro da kai, domin su kasance masu tarbiya a cikin al’umma da kuma tsayawa da kafafunsu.
Gwamnan ya tabbatar da haka ne a ranar Talata a filin wasa na Sani Abacha, a yayin wani horo da aka shiryawa Tubabbun ‘yan daba guda 222 da rundunar yansandan jihar kano ta shirya.
Wasu Tsaffin Gwamnonin PDP Tare Nyesom Wike Sun Gana Da Shugaban Kasa
Sanarwar da kakakin gwamnan jihar Kano Sanusi Bature ya fitar, ta Ambato gwamnan na jihar kano na cewar akwai shiri a kasa, na koyar da matasan sana’oin dogaro da kai da kuma masu tallafin karatu.
Ya kuma godewa kwamishinan yansandan jihar kano Muhammad Usaini Gumel saboda horon da aka shiryawa matasan da suka tuba daga aikata lefuka.
A Wani labarin kuma Wasu Tsaffin Gwamnonin PDP Tare Nyesom Wike Sun Gana Da Shugaban Kasa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
