Connect with us

News

Wasu Tsaffin Gwamnonin PDP Tare Nyesom Wike Sun Gana Da Shugaban Kasa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Ministan Abuja Nyesom Wike ya jagoranci tawagar tsaffin gwamnonin guda hudu da kuma guda daya dake kan mulki a halin yanzu, inda suka gana da shugaban kasa Bola Tinubu a daren jiya.

Rahotanni sun baiyana cewar an fara yin ganawar ne a gidan minista Wike dake Abuja, kafin daga bisani su garzaya wajen shugaban kasa Bola Tinubu a fadarsa dake Villa Abuja.

Kungiyoyin Kwadago Na Kasa Sun Baiwa Gwamnoni Wa’din Mako Biyu Domin Fara Biyan Karin Albashi Na Dubu 35

Duk da cewar babu bayanin abunda ganawar ta kunsa, sai dai wasu rahotanni na baiyana cewar ganawar tasu bata rasa nasaba da inganta alaka tsakanin tsaffin gwamnonin da kuma shugaban kasa.

A wani labarin kuma Kungiyoyin Kwadago Na Kasa Sun Baiwa Gwamnoni Wa’din Mako Biyu Domin Fara Biyan Karin Albashi Na Dubu 35

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending