News
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta karyata rade-radin da ke nuna shakku kan allurar cutar mashako
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta karyata rade-radin da ke nuna shakku kan lafiyar allurar cutar mashako, a aikin rigakafin da ake gudanarwa a jihar.
A wata tattaunawa da manema labarai da Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf da aka yi a yau da sashin hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ya bibiya, Kwamishinan ya ce ikirari da wasu mutane ke yi na cewa allurar na da hadari ba gaskiya ba ne, saboda akwai kurakurai a ikirarin nasu.
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf Zai Samar Da Sana’oin Dogaro Da kai Ga Tubabbun Masu Aikata Lefi
Dakta Labaran yana mayar da martani ne ga wani faifan sauti da ke yawo a kwanakin nan inda wasu mata ke danganta allurar cutar mashako da illa ta yadda, kamar yadda suka yi zargi, ya sa ‘ya’yansu na fama da matsalar koda.
Ya ce da farko daya daga cikin masu korafin ta bayyana cewa shekararta 23 kuma an yi mata allurar, wanda ba gaskiya ba ne, domin ba a yi wa manya allurar, yara ‘yan shekaru 14 zuwa kasa kadai ake yi wa.
Haka kuma, a cewar Kwamishinan, masu ba da alluran rigakafin ba sa zuwa wuraren wasa, kamar yadda daya daga cikin matan ta ambata, don yi wa yara allurar; an zaunar da su a wuraren da aka tana inda mutane ke kawo ’ya’yansu domin a yi musu allurar.
“Saboda wadannan dalilai guda biyu, na yi imani da cewa abin da matan ke fada gaba daya karya ne. Amma, mai yiyuwa ne wanda aka yi wa kowace irin allurar rigakafi ya samu ciwon kai da zazzabi masu sauki. Rigakafin mashako na iya haifar da zafi da kumburi a wurin da aka yi allurar, da zazzaɓi, da ciwon kai, wani lokacin kuma da raunin jiki. Ko da su din ma ba da wuce sa’o’i 24”, ya fayyace.
Ya bayyana cewa ya binciki lamarin inda ya gano cewa wadannan yaran suna fama da zazzabin cizon sauro a lokacin da aka yi musu allurar rigakafin cutar, inda ya ce bincike ya nuna iyayensu sun kai su cibiyoyin lafiya domin kula da lafiyarsu.
“Ya kamata mutane su fahimci cewa zazzabin cizon sauro yana haifar da cutar karancin jini mai tsanani. Wani bangare na rayuwar kwayoyin halittar da ke haifar da zazzabin cizon sauro na zama a cikin jajayen kwayoyin halittar jini. A lokacin da suka balaga, sukan fashe su fasa kwayoyin halittar. Idan mafi yawan kwayoyin halittar sun samu illa, za su halaka su kuma haddasa mutum ya iya kamuwa da cutar karancin jini da har ma ya buƙaci ƙarin jini.
“Ya kamata mutane su sani cewa zazzabin cizon sauro yana shafar koda, matsanancin zazzabin cizon sauro na iya haddasa gazawar koda, amma ba rigakafin mashako ba idan ma har an yi wa mutum rigakafin. Mun ba da alluran nan sama da miliyan biyu, kuma ba mu taba samun rahoton wani mummunan sakamako ba game da alluran rigakafin,” Dr. Labaran ya jaddada.
Daga nan sai ya tunatar da jama’a cewa an shafe shekaru a cikin al’umma, saboda ita ce allurar da ake yi wa yaratsawon shekaru da dama, ya mai nuni da cewa abin da ke faruwa a yanzu shi ne bullar cutar mashako a Kano inda aka kawo alluran rigakafi da dama a jihar don ragewa da dakile yaduwarta.
Kwamishinan ya kuma tunatar da jama’a cewa tun farko ana kiran allurar da DPT da yanzu an fi sani da Penta da ake yi wa yaran ma da ba su kai shekara daya ba, yana mai jaddada cewa duk mutumin da aka yi wa cikakkiuar allurar rigakafin a jihar Kano a lokacin yana karami, to tabbas an yi masa DPT/Penta sau uku.
“Bari in yi amfani da wannan dama wajen sanar da jama’a cewa mun hadu da matsalar allurar rigakafi da aka saba yi a jihar. Gwamnatin jihar Kano ta wancan lokaci ba ta yi wa ‘ya’yanmu rigakafi ba har tsawon watanni 18 zuwa 9. Wannan shi ne babban dalilin tashin hankalin da muke gani a yau na cutar mashako a Kano.
“Da ace wadancan yaran sun samu isasshen alluran rigakafi a cikin watanni 18 da suka gabata, da ba za mu fuskanci matsalar da muke fama da ita a yanzu ba. Wannan dalilin da ya sa kashi 80 na masu fama da cutar a kasar nan a jihar Kano suke.
“Abin takaici, mun kawo alluran rigakafin, kuma wani yana ikirarin cewa ba su da matsala. Wannan ikirari ba gaskiya ba ne,” in ji Dakta Labaran.
