News
Shirye-Shiryen Bikin Auren Zawarawa Na 2023 Na Cigaba Da Kankama A Jihar Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin jihar Kano tace tana cika alkawarin da ta dauka na daukar nauyin Auren Zawarawa da samari dqa ‘yan mata yayin da hukumar Hisbah ta jihar ta sayo kayan daki da kayan abinci da kayan sawa domin bikin auren.
Hukumar ta ce ta kashe sama da Naira miliyan 800 wajen sayen kayayyakin a wani bangare na shirye-shiryen daurin auren, mutane sama da dubu 1.
Kasheem Shettima ya buƙaci NAHCON da ta sake duba tsarin ciyar da Alhazai a ƙasa mai tsarki
Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya tabbatar da haka a lokacin da yake duba kayayyakin.
Ya ce amare zasu samu kayan daki da katifa da matashin kai, da kuma jarin Naira dubu 20 domin fara kasuwanci.
A cewarsa, irin wannan karamci zai taimaka matuka wajen dakile munanan dabi’u a cikin al’umma.