News
zabtarewar kasa na barazana ga rayuwar al’ummar Jigawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Zaizayar kasa na barazanar korar al’ummar da ke Karamar Hukumar Garki a Jihar Jigawa.
Malam Musa, wani mazaunin garin ya shaidawa Jaridar DAILY POST cewa sama da shekaru 40 garin yana cikin barazanar zabtarewar kasa sakamakon zaizayar kasa.
A cewarsa, “yanayin na kara fadada a lokacin damina kuma ya yi sanadiyar kashe gonaki da dama.
Rahotanni na nuni da cewa sun cikin hadarin rasa gidajenmu da filayen noma idan ba a dauki matakin gaggawa ba
Musa ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su gaggauta ceto mazauna yankin daga asarar gidajensu.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan FERMA, Sanata Babangida Hussaini tun da farko a lokacin da yake duba yankin, ya ce tuni gwamnati ta samar da injina don magance matsalar.