Connect with us

News

Kotu ta dakatar da korar da aka yiwa Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP

Published

on

Kwankwaso
Spread the love

DAGA Muhammad Muhammad Zahraddin

 

Wata babbar kotu a Kano ta ba da umarnin wucin gadi da ke hana korar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Advertisement

Jaridar Indarank  ta rawaito Kotun wadda Mai shari’a Usman Mallam Naabba ke jagoranta ta yanke hukuncin ne game da wata buƙatar wucin gadi, inda ta jingine dakatarwar da aka ce an yi wa Sanata Rabi’u Kwankwaso a matsayin ɗan jam’iyyar NNPP, kuma kada hukumar zaɓe ta amince da dakatarwar da ake cewa an yi masa har zuwa lokacin da kotun za ta saurari ƙarar ta kuma yi nata hukunci.

Baza’a haska fuskar alkalai da zasu karanta hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa ba a yau.

Takardar kotu ta bayyana cewa waɗanda ake ƙara sun haɗar da Cif Boniface Aniebonam da Gilbert Agbo Major da Barista Tony Christopher Obioha da Kwamared Ogini Olaposi da Hajiya Rekia Zanlaga da Mark Usman da Umar A.Jubril da Alhaji Adebanju Wasiu.

Advertisement

Sai dai, rahotanni na ambato ɓangaren da ake ƙara na jam’iyyar NNPP a ƙarƙashin jagorancin Gilbert Major Agbo na sanar korar ɗan takarar shugaban ƙasar nasu daga NNPP.

Ɓangaren dai ya ɗora alhakin korar a kan ayyukan zagon ƙasa ga jam’iyyar da kuma ɓarnatar da kuɗin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.

 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *