News
Mutane 30 Sun Mutu A Wurin Hakar Ma’adinai Dake Abuja
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mutane 30 ne suka mutu sakamakon ruftawar kasa da aka samu a wani wurin hakar ma’adinai dake yankin Kuje Abuja, A yayin da ‘yan bindiga suka sace mutane 19 a yankin Bwari dake birnin taraiyyar duk a ranar Alhamis.
An baiyana haka ne a yayin wani taro da aka yi jiya tsakanin ministan birnin taraiyya Abuja Nyesom Wike, da kuma shugabannin kananan hukumomin Abuja guda shida, Tuni dai ministan ya umarci shugabannin suyi gaggawar kafa kwamitocin karkatakwana domin saka ido kan aiyukan masu hakar ma’adinan.
Shugaban karamar hukumar Kuje, Abdullahi Sabo, Ya koka da aiyukan masu hakar Ma’adinan ta barauniyar hanya, Inda yace lasisin hakar ma’adinai da ake baiwa ‘yan kasar China na haddasa matsala ta rashin tsaro.
Daga nan ministan ya yi alkawarin ganawa da ministan kula da Ma’adinai na kasa, Dele Alake, domin magance aiyukan masu hakar ma’adinai ta barauniyar hanya a Abuja. Haka zalika ya yi alkawarin ganawa da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kwamishinan yansandan Abuja domin tattauna yadda za’a kubutar da mutanen da aka sace.
Wani labarin kuma Rundunar Yan sanda Sun Dakile Rikici A Cikin Kasuwar Abuja
Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya dawo gida Najeriya bayan dogon hutun da ya dauka domin duba lafiyarsa a kasar Jamus.
Gwamnan ya bar Najeriya watanni ukku da suka gabata domin duba lafiyarsa a kasar ta Jamus.
Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jihar Ondo, Wole Ogunmolasuyi, wanda ya tabbatar da dawowar gwamnan ga wakilinmu, Ya ce a yanzu haka gwamnan yana gidansa dake birnin Badun.
Kazalika maid akin gwamnan, Uwargida Betty ta tabbatar da dawowar mai gidan nata a shafinta na X, inda ta wallafa hotonsa a cikin jirgin sama.