News
Rundunar Yan sanda Sun Dakile Rikici A Cikin Kasuwar Abuja
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis ta ce ta dakile wani mummunan lamari a kasuwar Garki da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya a unguwar.
A cewar sanarwar da kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Haruna Garba ya fitar, an samu hatsaniya tsakanin ‘yan kasuwar da wasu mutane, ciki har da jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kuma wani tela mai suna Muhammad Habibu inda aka harbe-harbe.
Gamayyar Kungiyaar CODDAE Ta Kudiri Aniyar Maka Najeriya A Kotu
A cewar sanarwar, an samu nasarar kwato makaman da aka yi amfani da su wajen hargitsin, kuma yanzu an dawo da zaman lafiya cikin Kasuwar
Haka kuam Channels ta rawaito cewa Kwamishinan babban birnin tarayya Abuja ya kuma ja kunnen ‘yan kasuwar da su guji yin barna a dukiyoyin jama’a, musamman abin da ya shafi jami’an tsaro da ke wurin domin kare lafiyarsu.
Wani labarin kuma Gamayyar Kungiyaar CODDAE Ta Kudiri Aniyar Maka Najeriya A Kotu
Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.
Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.
Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.
Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.