Connect with us

News

Gwamnatin jihar Kano ta ce za’a dawo da ƙarɓar Harajin kullum-kullum na matuƙa Baburan Adaidai Sahu

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI. 

Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Engr. Muhammad Diggol ne ya bayyana haka a yammacin jiya Juma’a a helkwatartar Hukumar KAROTA

Da yake ganawa da Ƙungiyoyin sufurin Adaidai Sahu na jihar nan, ya ce ya zama wajibi Gwamnatin ta ci gaba da karbar harajin ga matuƙa Adaidai Sahu domin ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba

Advertisement

Sojojin Najeriya sun kashe ‘Yan ta’adda 817 da kama sama da dubu 1 cikin watanni 3

Kwamishinan ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za’a sabunta rijistar Adaidaita Sahu domin tantance matuƙan, tare da sanin adadinsu a faɗin jihar Kano

Yace za’a ɓullo da sabbin tsare-tsare waɗanda za su sauƙaƙawa matuƙan biyan harajin kullum-kullum tare da sabunta rijistar ba tare da an musguna musu ba, duba da yanayin da ake ci na matsayin rayuwa

Ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta san mutanen da suke tuƙa Adaidai Sahun duba da yanayin da ake ciki. A don haka ko wanne matuƙi dole ne sai ya samu shaidar sa hannu daga Mai Unguwarsa kafin a yi masa rijistar, hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a fadin jihar nan baki daya

Advertisement

A nasa jawabin Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir yace sun kula da yadda siyasa ta lalata ɓangaren sufuri a fadin jihar nan, a don haka ba za su zuba ido su bar ɓarakae ta ci gaba da faɗaɗa ba, dole ne a dauki matakin ɗinkin ɓarakar

Ya ja hankalin ƙungiyoyin Adaidai Sahun su haɗa kansu su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya domin cin gajiyar tsare-tsaren da gwamnati ke shirin bijiro da shi da manufufinta na ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba

Taron ya samu halartar Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Engr. Muhammad Diggol da shugaban Hukumar KAROTA Engr Faisal Mahmud Kabir da mai bawa Gwamna Shawara a ɓangaren sufuri na jihar Kano Maisalati Garko da kuma kungiyoyin Adaidai Sahu baki ɗaya

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *