News
Hatsarin kwale-kwale ya hallaka akalla mutum 36 a Neja da Adamawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumomi a kasar nan sun tabbatar da mutuwar akalla mutum talatin da shida sakamakon hatsarin kwale-kwale a jihohin Neja da Adamawa.
Gwamnatin jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya ta tabbatar da rasuwar akalla mutum 26 sakamakon kifewar kwale-kwale a karamar hukumar Mokwa ranar Lahadi.
Koda An Gyara Matatun Man Fetur Ɗin Najeriya, Mai Ba Zai Sauko Ƙasa Da 200 – IPMAN
Kakakin gwamnatin jihar Bologi Ibrahim ya ce mutane da dama sun bata sakamakon hatsarin kwale-kwalen wanda ke dauke da fiye da mutum 100, cikinsu har da mata da kananan yara.
A cewarsa, mutanen suna kan hanyarsu ce ta zuwa gona yayin da lamarin ya faru.
“An tabbatar da mutuwar akalla mutum ashirin da shida, yawancinsu mata da kananan yara, yayin da aka ceto fiye da 30, kuma yanzu haka gamayyar ‘yan sanda da masunta da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja suna ci gaba da neman wadanda lamarin ya rutsa da su,” in ji shi.
A nata bangaren, hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar akalla mutum goma a hatsarin kwale-kwalen da ya faru a Kogin Njuwa da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.
Shugaban hukumar Aminu Sulaiman ya ce an ceto mutum 10. Kwale-kwalen da ya kife ranar Juma’a yana dauke da akalla mutum 23 da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwa, in ji shi.
Nijeriya ta dade tana fama da hatsarin kwale-kwale, wanda hukumomi suka ce yana faruwa ne sakamakon daukar mutane fiye da kima da kuma rashin ingancin kwale-kwalen.
A watan Yulin da ya gabata, fiye da mutum 100 ne suka mutu sakamakon kifewar da kwale-kwale
Wani labarin kuma Koda An Gyara Matatun Man Fetur Ɗin Najeriya, Mai Ba Zai Sauko Ƙasa Da 200 – IPMAN
Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya dawo gida Najeriya bayan dogon hutun da ya dauka domin duba lafiyarsa a kasar Jamus.
Gwamnan ya bar Najeriya watanni ukku da suka gabata domin duba lafiyarsa a kasar ta Jamus.
Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jihar Ondo, Wole Ogunmolasuyi, wanda ya tabbatar da dawowar gwamnan ga wakilinmu, Ya ce a yanzu haka gwamnan yana gidansa dake birnin Badun.
Kazalika maid akin gwamnan, Uwargida Betty ta tabbatar da dawowar mai gidan nata a shafinta na X, inda ta wallafa hotonsa a cikin jirgin sama.
