Connect with us

News

Olusegun Obasanjo Ya Bukaci Gwamnati Ta Tallafawa Masana’antu

Published

on

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya baiyana bukatar dake akwai ga gwamnati kan ta karfafa gwiwar masu masana’antu da kuma kananan yan kasuwa domin dakile shigo da kayayyaki a kasar nan.

Ya baiyana haka ne a birnin Abeokutan jahar Ogun ya yin da yake gabatar da jawabi kan rawar da masu kananan kasuwanci ke takawa a bangaren masana’antu da kuma hana shigo da kayyaki, yayin bude wani kanfanin kera kujerun alfarma mai suna Olatunde Pristige Chairs Limited.

Advertisement

Jam’iyyar APC Ta Ce Zafin Shan Kaye Ne Ke Damun Atiku

Taron wanda ya samu wakilcin mai dakinsa Bola Obasanjo, Ya baiyana muhimmanci da masana’antu ke dashi a bangaren ciyar da tattalin arzikin kasa gaba da kuma samar da aiyukan yi ga dimbin matasa.

A Wani labarin kuma Jam’iyyar APC Ta Ce Zafin Shan Kaye Ne Ke Damun Atiku

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending