News
Tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ke cika shekaru 13 da rasuwa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A yau ne tsohon shugaban ƙasar Nigeria marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’adua ke cika shekaru 13 da rasuwa.
Umaru Musa Yar’adua ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayu shekarar 2010 a fadar Asorok dake Abuja bayan ya dawo daga dogon jinya a ƙasashen waje, inda mataimakinsa Dr. Goodluck Jonathan ya maye gurbinsa.
Kamfanin jirgin sama na Rano Air ya sanar da ranar fara zirga-zirga.
Umaru Musa Yar’adua ya mulki Nigeria tsakanin ranar 29 ga watan Mayu shekarar 2007 zuwa ranar 5 ga watan Mayu shekarar 2010
Shine ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 21 ga watan Afrilun shekarar 2007, inda ya kada abokan takararsa Irin su Muhammadu Buhari na jam’iyyar ANPP da ATIKU ABUBAKAR na jam’iyyar ACN.
An haifeshi a ranar 16 ga watan Agusta shekarar 1951 a garin Katsina. Ya kuma halarci kwalejin Barewa da Jami’ar Ahmadu Bello duk a birnin Zaria dake jihar Kaduna.
