Connect with us

News

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta tsaurara tsaro a gidan Messi da na Neymar saboda masu zanga-zanga

Published

on

 

 

Advertisement

Kungiyar kwallon ƙafa ta PSG ta ƙara jami’an tsaro a gidajen Messi da Neymar biyo bayan zanga-zangar da magoya baya ke yi suke gudanar wa

 

Advertisement

Ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasanni uku da ta buga cikin shifa a Lig 1, kuma tuni aka cire su daga gasar Champions.

Shekara Kwana: Shekaru 21 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano 

Magoya bayan ƙungiyar sun taru a ƙofar gidan Neymar ranar Laraba sun ihun sai ya bar ƙungiyar.

Advertisement

 

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta yi Allah-wadai da wannan lamari kuma ba za ta amince da ci gaban hakan ba.

Advertisement

 

Shi kuwa ɗan wasan Argentina Lionel Messi mai shekara 35 zai bar ƙungiyar ne a ƙarshen wannan kakar, wanda a yanzu haka yake fuskantar hukuncin dakatarwa ta mako biyu a ƙungiyar saboda ziyarar da ya kai Saudiyya ba tare da izini ba, shi ma na fuskantar ihu sakamakon laifin da ya yi.

Advertisement

 

A watan Maris ne ɗan wasan gaban Brazil Neymar ya samu rauni wanda ya sa ba zai sake buga wasa ba har ƙarshen kaka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending