Connect with us

News

Zulum Ya Bayar Da Umarni A Binciki Gawar ‘Yar Dan Majalisa Da Aka Kashe A Maiduguri

Published

on

 

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Fatima Bukar, ‘yar dan majalisar dokoki a jihar Borno, Bukar Abacha, mai wakiltar mazabar Ngala, wasu da ba a san ko su wanene ba a ranar Talata, sun kashe ta a yankin Dikechiri Bayan Gidan Dambe da ke a garin Maiduguri a cikin jihar Borno.

Mijin mariganyiyar ne ya dauki gawarta ya kai ofishin ‘yansanda da ke Gwange, inda ya ce, ya iske gawarta ne a gidansa, inda aka daure hannayen ta da kafuwanta, kana kuma ‘yar mariganyiyar mai shekaru biyu da haihuwa, tana kuka.

Shakku A Kan Zaɓukan 2023: Ana Taƙaddama Game Da Kashi 94 Cikin 100 Na Kujerun Da Aka Lashe

Jami’an ‘yansandan, daga nan sai suka dauki gawawarta suka kai dakin adana gawarwaki na asibin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

Advertisement

Leadership ta rawaito cewa Lamarin ya jefa fargaba ga mazauna yankin, wanda hakan ya janyo mutane suka ta zuwa gurin da abin ya afku don ganewa idanuwansu. .

Bugu da kari, rundunar ‘yansanda ta jihar, ta cafko mijin mariganyiyar, Adam Alhaji Ibrahim.

Wata majiya kusa da dangin mariganyiyar ya ce, an kama Adam ne a daren ranar Talata bayan gwaman jihar, Babagana Umara Zulum ya umarci mahukunta su kai gawar Fatima zuwa asibitin kwararru don a gudanar da bincke akan gawarta.

Iyayanta da sun tsara za su yi mata jana’iza a ranar Laraba domin a bizne ta da misalin karfet 2 na rana a rukunin gidaje 707 da ke a Maidugur,

A wani labarin kuma Shakku A Kan Zaɓukan 2023: Ana Taƙaddama Game Da Kashi 94 Cikin 100 Na Kujerun Da Aka Lashe

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

 

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

 

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

 

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending