Connect with us

Entertainment

Za,a Saki Gawurtaccen Fim Din Nan LULU DA ANDALU Season 2 A Watan January 2024 

Published

on

Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Kamfani shirya fina finan Hausa na Blue Sound Multimedia zarce tunanin masu tunani, musamman wanda yasan yadda kamfanin ya fara sama da shekaru

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa tayi imanin wani zai gaskata abinda ta fada na cewar an samu cigaba kwarai da gaske wanda hakan yasa duniya tasan da zaman shahararren fim din LULU DA ANDALU daya bunkasa nagartattun fina-finan da ake samarwa duk kuwa da kalubalan kudi sakamakon karancin samun tallafi ko zuba jari daga bangaran gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin film.

Muslim Yunus Abdullahi ya taya Sanata Kwankwaso murnar cika shekaru 67 a duniya

Haka kuma shirin LULU DA ANDALU din ya nuna yadda dangantaka da mu’amular rayuwa ke gudana tsakanin bil’adama da ‘Jinnu” ta yadda mutane da aljanu za suyi aiki tare wajan gano maboyar da aka killace tarin dukiyar, inda bil’adama da jinnu za suyi amfani da tsafi wajan gudanar da aikinsu.

Haka kuma wannan shirin yasa mu lambar yabo ta musamman na Fim na ƙasa da kasa na 2023 daga Kaduna International Film Festival karu na shida

Advertisement

 

 

MANSA MUSA wani shaharerren mai dukiya ne dan kasar MALI wanda tarihi ya tabbatar da cewa ya taba zama mutumin da babu wanda ya kaishi tarin dukiya a fadin duniya, yayi mulkinsa a matsayin MANSA na MALI tsakanin shekara ta 1312 sannan kuma ya rasu a shekara ta 1337.

Advertisement

 

Sai kuma kwatsam a wannan zamanin namu na shekara 2022 aka sami wani bawan Allah wanda burinsa shi ne ya gano inda dukiyar MANSA MUSA take domin ya mallaketa, sai dai kafin gano inda dukiyar MANSA MUSA take dole sai an taso da wasu hatsabiban Aljanu guda biyu wato LULU da ANDALU daga wani dogon barcinsu na shekaru sama da 700 da suka gabata suna shekar kayansu.

 

Advertisement

 

 

Domin tabbatar da yuwar wannan aikin film, mashiryin Shirin film din Lulu da Andalu ya dauki kwararrun masana aikin shirya film da jarumai maza da mata domin tabbatar da ganin wannan gagarimin aiki ya zama gaskiya, Wanda zai gamsar da duniya makallata fina- finai a fadin Duniya.

Advertisement

Daga karshe dai Muna fatan ganin Gawurtaccen film zai gamsar da masu kallo na fadin Duniya, Wanda hakan zai janyo tafka muhawara a tsakanin jama’a.

 

Saboda haka mu jira fitowar wannan kayataccen shiri da zarar an Kamala aikinshi. Jin jina ga duk kanin masu ruwa da tsaki na Shirin LULU DA ANDALU.

Advertisement

Zai fara zuwar muku daga January 2024 a tashar AFRICA MAGIC HAUSA dake kan DSTV

Sai kuma tashar TY SHABA TV dake kan

YouTube

Advertisement

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *