News
Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC
DAGA. YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu ‘yan bindiga sun mamaye tsohon garin Zungeru na jihar Neja inda suka yi garkuwa da tsohon shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Wushishi, Alhaji Sule Muhammad.
A jiya ne ‘yan bindigar suka kai farmakin inda suka yi ta harbe-harbe kafin su daga bisani suka ranta ana kare.
Karancin Ruwan Sha Ya Kara Ta’azzara Cikin Wannan Shekarar A Garin Fika Na Jihar Yobe
Wasu mazauna unguwar da suka zanta da manema labarai sun ce an yi garkuwa da tsohon shugaban ne a gidansa da misalin karfe 12 na safiyar jiya yayin da ‘yan bindigar suka raunata ‘yarsa da dansa. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun amsa kiran waya da aka yi masa ba, sai dai an tura masa sakon karta kwana amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai ce komai ba dangane da wannan al’amari.
A wani labarin kuma Karancin Ruwan Sha Ya Kara Ta’azzara Cikin Wannan Shekarar A Garin Fika Na Jihar Yobe
Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce Hamas ta sako 24 a cikin mutanen da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza a yau.
A wani sako da ta wallafa a dandalin X, wani magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta ce rukunin wadanda aka sako din sun kunshi ‘yan Isra’ila 13 da ‘yan kasar Thailand 10 da kuma wani dan kasar Philippines daya.
Qatar ce ta shiga tsakani don cimma yarjejeniyar tsakanin Isra’ila da Hamas.
Tun farko, fira ministan Thailand ya ce ‘yan kasarsa mutum 12 Hamas ta sako.
