Sports
Man City da Tottenham sun tashi 3-3 a wasan mako na 14 a Premier League
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Manchester City da Tottenham sun tashi 3-3 a wasan mako na 14 a Premier League a Etihad ranar Lahadi
Tottenham ce ta fara cin kwallo ta hannun kyaftin, Heung-min Son a minti na shida da fara wasa, minti uku tsakani City ta farke, bayan da Son ya ci gida.
Kano Pillars ta lallasa Gombe United yayin da Yusuf Abdullahi ya ci kwallaye 5
Daga nan ne Phil Foden ya kara na biyu, haka suka je hutu City na cin 2-1.
Da suka koma zagaye na biyu Giovani Lo Celso ya farkewa Tottenham, sai dai Jack Grealish ya zura na uku a ragar Tottenham.
Daf da za a tashi wasan kungiyar Ange Posteglou ta farke ta hannun Dejan Kulusevski.
Da wannan sakamakon City ta koma mataki na uku a teburin Premier League da maki 30, Liverpool ce ta biyu mai maki 31, wadda ta doke Fulham 4-3 a Anfield ranar Lahadi.
Tottenham kuwa wadda aka doke wasa uku a jere kafin zuwanta Etihad ta yi kasa zuwa mataki na biyar da maki 27.
Arsenal ce ta daya a kan teburin Premier League da maki 33, bayan wasannin mako na 14.
