Connect with us

News

Kisan ’Yan Mauludi: Bala’in Ya Yi Wa ’Yan Arewa Yawa —Bello Yabo

Published

on

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Bello Yabo

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Bello Yabo ya bayyana alhilinsa kan yadda ake kashe al’ummar Arewacin Najeriya inda ya ce bala’in ya yi yawa.

Ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da yake tsokaci kan kisan da jirgin soya ya yi wa masu taron Mauludi a garin Tudun Biri a Jihar Kaduna.

Advertisement

Bournemouth ta kunyata Man United a Old Trafford

Malamin ya ce, “ga ’yan ta’adda sun addabi ’yan Arewa, ga yunwa sannan kuma ga sojoji na kisa da sunan kuskure.”

Don haka sai ya roki ’yan Arewa da su tashi tsaye su cire hassada da bakin ciki wajen kare martabarsu ta hanyar hada kansu, su rika magana da murya daya.

Advertisement

 

Lauyoyin Arewa za su maka gwamnati a kotu kan kisan Tudun Biri

Advertisement

“Allah Ya isar wa bayin Allah da aka kashe, Allah Ya gafarta musu.

“Wannan kisa Allah Ya sa ya zama kaffarar zunubansu, Allah Ya sa iyakan wahalarsu ke nan.

Advertisement

“Amma tsakani da Allah bala’i ya yi mana yawa mu ’yan Arewa. Jama’a ’yan ta’adda su kashe mu, yunwa ta kashe mu, Sannan kuma sojojin da ya kamata su kare mu da dukiyarmu su zo suna kashe mu.

“Zafin ya yi mana yawa, bala’in ya yi yawa. Wa za ka fada wa in ba Allah ba?

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending