Sports
Victor Osimhen ne gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2023
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar ƙwallon Afirka ta Caf ta sanar da ɗan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, a mastayin gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2023.
Caf ta sanar da Osimhen ne a taron karrama gwarazan ‘yan ƙwallon nahiyar na 2023 da ke gudana yanzu haka a birnin Marrakesh na Moroko.
Ɗan ƙwallon mai shekara 24 ya taimaka wa ƙungiyarsa Napoli ta Italiya wajen lashe kofin Serie A, da kuma cin ƙwallaye mafiya yawa a kakar 2022-23.
Shi ne ɗan wasan Najeriya na farko da ya lashe kambin cikin shekara 24, bayan Nwankwo Kanu ya lashe ta a shekarar 1999.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News5 days ago
Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna
