Sports
Alƙalin wasa ya sha naushi daga shugaban wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Jami’ai a Turkiyya sun ce suna ɗaukar mataki na magance duk wata matsala a ɓangaren wasannin kwallon ƙafa ta hanyar dakatar da dukkan wasu wasanni a ƙasar.
Hakan ya biyo bayan naushi da aka yi wa ɗaya daga cikin manyan alƙalan wasan ƙasar bayan wasan da aka yi a jiya Litinin.
Halil Umut Meler, ya sha naushi daga shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar ta MKE Ankaraguju, bayan sun faɗi a wasan da aka yi a gasar Super Lig Clash.
Kazalika magoya bayan ƙungiyar ma sun daki alkalin wasan wanda aka garzaya da shi asibiti don yi masa magani.
Wakilin BBC ya ce abin da ya faru a daren Litinin ya janyo tashin hankali wanda ya haɗa da ‘yan wasa da ‘yan kallo a inda aka kama mutane da dama a filin wasan.
Shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan na daga cikin wadanda suka yi alawadai da abin da aka yi.
-
News24 hours ago
Rundunar ‘Yansanda Ta Yi Gargaɗi Gam Da Yiwuwar Kai Hare-hare Makarantu Da Wuraren Ibada
-
News5 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News6 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
