News
Wata Sabuwa, Gwamnatin Ribas ta Fara Ruguje Ginin Majalisar Dokokin Jihar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rikicin siyasar jihar Ribas ya dauki sabon salo a safiyar yau Laraba yayin da gwamnatin jihar ta fara rusa majalisar dokokin jihar.
Channels TV ta tattaro cewa kimanin Motocin rusau 10 ne suka shiga harabar majalisar a daidai lokacin da wasu ‘yan majalisar masu biyayya ga gwamnan jihar, Sim Fubara suka yi zaman farko.
Jirage Zasu Rika Biyan Diyya Ga Fasinjojin Da Suka Yi Jinkirin Tashi -Ministan sufurin jiragen sama
Zauren Majalisar ya samu halartar Masu biyayya ga Gwamnan Jihar Mai Ci wanda shugaban bangaren Edison Ehie ya jagoranta.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito a ranar Talata cewa babbar kotun jihar Ribas ta bayar da wani tsohon umarni na amincewa da Edison Ehie a matsayin sahihin kakakin majalisar dokokin jihar Ribas.
Bangaren kakakin Majalisar, Ehie, a yayin zaman, ya bayyana cewa ginin ya kamata a gyara bayan fashewar da ta afku a ginin a ranar 30 ga watan Oktoba, 2023, yana mai cewa gwamnan zai samar musu da wani wurin da za su zauna kafin nan.
Idan dai ba a manta ba, Majiyar mu ta rawaito a ranar Litinin din da ta gabata cewa ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas su 27 masu biyayya ga tsohon gwamna kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, sun fice daga jam’iyyar PDP mai mulki, inda suka koma jam’iyyar adawa ta APC a jihar
-
News17 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
