Connect with us

News

Gwamatin Tarraya za ta raba Hukumar Bada Wutar Lantarki, TCN gida biyu

Published

on

 

 

Advertisement

Gwamnatin tarraya za ta raba Hukumar Bada Wutar ta Ƙasa gida biyu.

A wata sanarwar da aka nuna alamun yin haka, TCN, wato ‘Transmission Company of Najeriya, za a raba shi zuwa gida biyu.

Advertisement

Wata Sabuwa, Gwamnatin Ribas ta Fara Ruguje Ginin Majalisar Dokokin Jihar

Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke magana a taron Sanin Makamar Aiki na Ma’aikatar sa, wanda ya gudana a ranar Talata, a Abuja.

Kamfanin TCN wanda shi ke tafiyar da aikin raba wuta, ya na ɗaya daga cikin kamfanoni 18 da aka samar daga kamfanin samar da wutar lantarki na PHCN cikin Afrilu, 2004.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa TCN ya zama cikakken kamfani cikin Nuwamba, 2005 kuma a cikin shekarar ce aka ba shi lasisin amincewa ya samarwa da raba wutar lantarki.

Kamfanin dai a zaman yanzu mallakin Gwamnatin Tarayya ne.

Advertisement

Adelabu ya ce za a yi wa TCN garambawul, inda za a raba shi gida biyu, wato ISO, mai zaman kan sa da kuma TSP.

Ya ce, “tilas ne mu yi nazarin shin gwamnati ce za ta samar da wuta a ƙasa baki ɗaya, ko kuwa dai kawai damar samar da wuta a ƙasa baki ɗaya za ta bayar.

Advertisement

Ya yi maganar cewa hakan zai bunƙasa samun hasken lantarki a yankunan karkara da kuma faɗin ƙasar nan.

Najeriya na fama da matsalar wutar fiye da shekaru 30. Wannan kuwa ya haifar da ambaliyar janareto-janareto manya da ƙanana, da kuma yawan amfani da hasken rana domin a samun hasken sola.

Advertisement

Haka kuma matsalar ƙarancin wutar lantarki ya haifar da tsadar rayuwa, saboda yawancin ababen da masana’antu manya da ƙananan ke sarrafawa duk san yi tsada.

A cikin 2023, tashar samar da wutar lantarkin Najeriya ta durƙushe sau shida.

Advertisement

A wani labarin kuma Wata Sabuwa, Gwamnatin Ribas ta Fara Ruguje Ginin Majalisar Dokokin Jihar

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending