Connect with us

News

2024 :  Gwamna Sanwo-Olu ya gabatar da kasafin Kudi na tiriliyan 2.2 ga majalisar dokokin jihar.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a ranar Laraba ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 na naira tiriliyan 2.2 ga majalisar dokokin jihar.

Kasafin kudin mai taken ‘Budget of Renewal’ an gabatar da shi ne a dakin taro na majalisar dokokin jihar Legas da ke Alausa, Ikeja.

Advertisement

Wata Sabuwa, Gwamnatin Ribas ta Fara Ruguje Ginin Majalisar Dokokin Jihar

Kasafin kudin da aka gabatar ya kunshi kashe kudi na yau da kullun na Naira tiriliyan 1.02, wanda shine kashi 45 cikin 100 na jimillar kasafin kudin, da kuma kashe naira tiriliyan 1.22, wanda shine kashi 55 cikin 100 na kasafin kudin.

Gwamnan ya yi nuni da cewa kudirin na shekarar 2024 zai kara rage illar kawar da tallafin man fetur da sauran matsalolin tattalin arziki ga mutanen Legas.

Advertisement

Daily Post ta ruwaito cewa Ya ce tsarin hada kasafin kudin ya gudana ne a karkashin tsarin gwamnatinsa na T.H.E.M.E.+, wanda a cewarsa, ya fara gina kasafin kudin gwamnatin sa a baya tun lokacin da aka zabe shi a shekarar 2019.

Sanwo-Olu ya kara da cewa kasafin kudin zai karfafa nasarorin da gwamnatin sa zata samu.

Advertisement

Da yake magana kan yadda kasafin kudin shekarar 2023 ke gudana, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da kashi 78 cikin 100 na shekarar 2023 a cikin kwata uku kuma ya yi hasashen cewa za a iya aiwatar da akalla kashi 98 cikin 100 nan da karshen shekara.

Ku tuna cewa gwamnatin jihar ta amince da kasafin Naira tiriliyan 1.768 na kasafin kudin shekarar 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending