Connect with us

News

Hukumar NAHCON Ta Dakatar Da Rabon Kujeru Ga Kamfanonin Jirgin Yawo

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

 

Advertisement

Hukumar Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) a dakatar da rabon kujeru aikin Hajjin 2024 ga kamfanonin jirgin yawo 40 da suka yi nasarar samun aikin jigilar maniyyata.

Hukumar NAHCON ta dakatar da rabon kujerun ne saboda korafe-korafen da zargin rashin adalci da wasu kamfanonin da ba su yi nasara ba ke yi.

Advertisement

Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce hukumar na sane da irin wadanna zarge-zarge daga wasu kamfanonin da ba su yi nasara a tantancewar da aka yi ba.

Don haka aka dakatar da akain na tsawon awa 48 masu zuwa, domin daukar matakin da ya dace, tabbatar da tsafta a aikin da kuma kare martabar kukumar.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa Fatima Sanda ta ce shugaban Hukumar, Jalal Ahmad Arabi, ya ba da dama ga duk kamfanin da ke da sahihin korafi kan rashin dacewar wani daga cikin wadanda suka samu aikin, ya gabatar da hujjojinsa domin a dauki matakin da ya dace.

Ta bayar da tabbacin za a yi zuzzurfan bincike a kan duk zargin da aka gabatar a rubuce, domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon kujerun.

Advertisement

Kakakin ta NAHCON ta kara da cewa duk da haka, duk kamfanin da aka samu ya yi wa nai kage, zai fuskanci hukunci.

A wani labarin kuma Bankin Duniya Ya Shawarci Gwamnatin Tarayya Ta Maida Farashin Litar Man Fetur 750

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending