Connect with us

News

Da Ɗuminsa: Kotun koli ta tabbatar da tuhumar cin amanar kasa da ake yi wa Nnamdi Kanu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Kotun koli ta tabbatar da tuhumar cin amanar kasa da ake yi wa Nnamdi Kanu

A ranar Juma’a ne kotun koli ta amince da tuhumar cin amanar kasa da ake yi wa shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Advertisement

Kanu na hannun jami’an tsaro na farin kaya, DSS, tun bayan da aka sake kama shi a shekarar 2021.

Mutane 16 Sun Rasu, Wasu 30 Sun Samu Rauna A Hatsarin Tirela A Jos

A wani labarin kuma Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar

Advertisement

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli

Advertisement

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending