News
Kasafin Kuɗi Na Naira Tiriliyan 1.57 Ba Zai Isa Yaƙar Matsalar Tsaro Ba – Minista
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya roƙi Majalisar Tarayya da ta ƙara kasafin kuɗi da aka kasaftawa ma’aikatarsa na shekarar 2024, inda ya ce sam Naira Tiriliyan 1.57 da aka ware musu ba zai isa a yaƙi matsalar tsaro a kasar nan ba.
Ministan ya yi wannan kiran ne a ranar Larabar da ta gabata lokacin da ya gurfana gaban kwamitin haɗin gwiwa na majalisar domin kare kasafin kuɗin shekarar 2024 da aka warewa ma’aikatar.
Badaru ya ce hauhawar farashin kayan aiki da kuma ƙarin farashin man dizal da man fetur su ne dalilan da suka sanya ya nemi ƙarin kasafin.
Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta koma saman teburin firimiya bayan doke Brighton
An baiwa Ma’aikatar kasafin kuɗi kamar haka Naira Tiriliyan 1.15 ga ma’aikata; N116.5bn abin da aka ƙara sai kuma N308.2bn na uwar ƙudi wanda ya haɗa jimilar N1.57trn.
Sai dai duk da wannan tagomashin kuɗaɗe ministan tsaro ya ce wannan kason ba zai kai ko ina ba wajen yakar matsalar tsaro.
“Ina kira ga Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai da su sake duba wannan kasafin kudin bisa la’akari da yanayin yadda tattalin arzikin ƙasar yake.
Ministan ya ƙara da cewa Hafsun sojoji suna amfani da man fetur da dizal mai yawan gaske don gudanar da ayyukan su.
Wikki Time ta ruwaito cewa Ya kuma ba da tabbacin cewa duk kuɗaɗen da aka ware za a yi amfani da su yadda ya dace.
