News
Tikitin jiragen sama ya yi tashin da ba’a taba gani ba a Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Yayin da jama’a ke shirin fara tafiye tafiye domin halartar bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a garuruwansu.
Rahotanni na nuni da cewa farashin tikitin jiragen sama sun yi tashin da ba’a taba ganin haka.
Hukumar EFFC na bukatar majalisa tayi doka a kan masu zama attajirai dare guda
Rahotanni sun ce yanzu haka ana sayar da tikitin tafiya guda a kan naira dubu 200 a wasu hanyoyin da jiragen ke zirga zirga.
Wani binciken da Jaridar Daily Trust tayi ya bayyana cewar, duk da tsadar tikitin, tuni masu hannu da shuni suka saye wasu kujerun, domin kaucewa matsala a ranakun da suke shirin suyi tafiyar.
Jaridar tace binciken da ta gudanar ta bibiyan shafukan jiragen saman na nuna cewar, tuni aka sayar da tikiti da dama daga cikin jiragen da aka tsara za suyi zirga zirga a lokacin.
Sakamakon binciken ya nuna cerwar, matsalar tafi kamari a hanyar zuwa Enugu, inda ake sayar da tikiti guda a tsakanin naira dubu 171 zuwa dubu 200, yayin da tikitin zuwa Fatakwal daga Abuja yake tsakanin naira dubu 99 zuwa dubu 138.
Binciken yace tikitin tafiya Sokoto daga Lagos ya kai naira dubu 150, yayin da ake sayar da tikitin Kaduna a kan naira dubu 143, sai kuma Lagos zuwa Ilorin dake tsakanin naira dubu 100 zuwa dubu 143.
Wasu masana na danganta wannan matsalar da tsadar mai da jiragen ke amfani da su, wasu kuma na alakanta matsalar da rashin ingantattun hanyoyin mota, yayin da wasu ke danganta tsadar da matsalar tsaro, lura da yadda ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane ke yiwa jama’a illa a kan hanyoyin kasar.
A wani labarin kuma Hukumar EFFC na bukatar majalisa tayi doka a kan masu zama attajirai dare guda
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
