Connect with us

News

2023: Shekarar fara tonon silili, fallasa da tereren madaƙolon satar kuɗaɗe a shekaru 8 na gwamnatin Buhari

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Kamar yadda lokacin da tsohuwar gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ta sha fallasa da tonon silili da tereren satar maƙudan kuɗaɗe, lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya hau mulki a cikin 2015, to yanzu ma watanni kaɗan bayan saukar Buhari a 2023 an fara fallasa irin madaƙolon satar kuɗaɗen da aka riƙa yi a zamanin gwamnatin sa.

Tuni mutane irin Honorabul Gudaji Kazaure, wanda ya riƙa tona asirin manyan jami’an gwamnatin Buhari tun kafin saukar su, ya sake fitowa yanzu ya na jaddada cewa satar da aka ɗirka zamanin Buhari ta fi ta zamanin mulkin Jonathan nesa ba kusa ba.

 2023: Shekarar da Naira ta shiga sahun gaban kuɗaɗen da suka fi rashin daraja a duniya

Tun farko dai shekarar 2022 ta kasance Larabar fa aka fara fahimtar cewa Juma’ar ƙarshen mulkin Buhari idan ta zo cikin 2023, ba za ta yi kyau ba.

Ba wani abu ba ne ya fara nuna haka, sai yadda aka kama Akanta Janar na Tarayya na gwamnatin Buhari, wato Ahmed Idris ya saci sama da Naira biliyan 100, amma Buhari bai ma san an saci kuɗaɗen ba.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa tun Buhari na kan mulki ake zargin hadimin sa Sabi’u Tunde ya ƙazamce ta hanyar yin badali cikin tekun maƙudan kuɗaɗen al’ummar Najeriya, kuma kuɗaɗen ba ‘yan kaɗan ba. Har Buhari ya sauka ba a binciki Tunde Sabi’u ba.

Wata ɗaya bayan saukar Buhari daga mulki, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi cacukui da Godwin Emefiele, gogarman Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN da a yanzu ake ta binciken yadda ya sace kuɗaɗen ƙasar nan. Bincike ya nuna bai dai yi wa Najeriya ƙarƙaf ba, amma dai ya tsiyata ƙasar kuma ya jefa ‘yan Najeriya sama da miliyan 200 cikin ƙuncin rayuwa da raɗadin tsadar rayuwa.

Gararrumar satar kuɗaɗen Najeriya a ɓoye a bankuna cikin asusu sama da 593 a Amurka, Turai da Chana, wani ɓangare ne na madaƙolon satar kuɗaɗe a ƙarƙashin gwamnatin Buhari, wanda su Emefiele su ka yi.

Akwai kuma harƙallar buga sabbin launin kuɗaɗe, wadda ita ma wata gidoga ce mai zaman kanta.

An dai buga kuɗaɗen a Kamfanin Buga Kuɗaɗe da Takardun Sirri na Gwamnatin Najeriya, da ke Abuja, wato ‘Nigerian Printing and Minting Company’, wanda a lokacin da aka buga kuɗaɗen, ɗan uwan A’isha Buhari ne shugaban kamfanin buga kuɗaɗen.

Wannan badaƙala da ake bankaɗowa, duk somin-taɓi ce, domin ba a ma san abin da za a bankaɗo ba a cikin 2024 kenan.

Advertisement

Kada a manta, a cikin 2023 minista a ƙarƙashin mulkin Buhari, Hadi Sirrika wanda kusan ɗan uwan Buhari ne, domin shiyyar su ɗaya, a matsayin sa na Ministan Sufurin Jiragen Sama, ya shirya gadangarƙamar ƙaddamar da jiragen saman Nigerian Air, jiragen da ko ungulu ta fi su tasiri a tashi bisa sararin samaniya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending