Connect with us

News

Wata mata da miji sun shiga hannun hukuma kan zargin kashe wani a kasuwa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wata mata da miji sun shiga hannun hukuma kan zargin kashe wani wanda suka yi fada da shi a kasuwa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta damke wannan mata da miji ne bayan mutuwar abokin fadan nasu mai suna Mista Mark Kalu.

Advertisement

Yadda gwamnatin Kaduna ta dauki ma’aikata aiki a Jami’ar KASU, taki biyan su albashi na tsawon shekaru uku

A safiyar Lahadi ne kakakin rundunar, SP Omolola Odutola, ta sanar a Abeokuta cewa Mista Kalu wanda ya samu raunuka a sassan jikinsa a yayin fada da ma’auratan ya mutu.

SP Odutola ta ce, “Rikicin Mista Kalu da ma’auratan a kasuwa ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Advertisement

“Babaloja na Osiele da kuma shugabannin kabilar Igbo sun yi kokarin ganin an sasanta lamarin cikin ruwan sanyi.

“Amma dai yanzu wadanda ake zargin suna hannun ’yan sanda ana gudanar da bincike.”

Advertisement

Ta ce gawar mamacin kuma an kai ta Babbar Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Idi Aba, Abeokuta domin gudanar da bincike.

Aminiya ta ruwaito cewa Mata da mijin da ake zargin dai sun ba hamata iska da Mista Kalu ne a ranar 8 ga watan Oktoba 2023, a Kasuwar Osiele da ke Jihar Ogun.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending