Connect with us

News

Yadda gwamnatin Kaduna ta dauki ma’aikata aiki a Jami’ar KASU, taki biyan su albashi na tsawon shekaru uku

Published

on

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI

 

Advertisement

Wasu malamai da ma’aikata a Jami’ar jihar Kaduna KASU sun koka da yadda suka ɗauki tsawon shekaru uku suna aiki amma ko sisi ba a taɓa biyan su a matsayin albashi ba ballanta na alawus ko kudin hutu.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa wadannan ma’aikata sun bayyana cewa an cire sunayen su daga jadawalin sunayen ma’aikatan Jami’ar da ake biya albashi.

Advertisement

Yadda ‘Yan Najeriya Ke Kallon Alwashin Da Tinubu Ya Sha Na Inganta Wutar Lantarki

Ma’aikatan sun ce Jami’ar bata biyan su albashi saboda tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya maida al’amuran Jami’ar ƙarƙashin ofishin sa, komai za ta yi sai ya sa hannu.

Ma’aikatan sun ce basu cikin tsarin inshorar lafiya saboda basu da takardan shaidan biyan su albashi.

Advertisement

Wani cikin ma’aikatan da baya so a fadi sunnan sa ya ce ya yi watanni 22 yana aiki ba a biya shi albashi ba.

“Bayan an dauke ni aiki sai na samu karin girma zuwa matsayin mataimakin babban malami amma babu albashi. Daga nan wasu daga cikin mutanen da muka samu aiki tare suka fara samun albashi a watan Fabrairu amma mu kuma shuru.

Advertisement

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar Adamu Bargo ya ya ce jami’ar na karkashin ikon gwamnatin jihar Kaduna ne, gwamnatin ce ke biyan duk ma’aikatan jami’ar albashi kamar yanda Jaridar premium Times ta ruwaito 

Bargo ya yi kira ga duk ma’aikatan da basu samun albashi da su kara hakuri cewa jami’ar na kokarin warware wannan matsala nan ba da dadewa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending