News
Muslim Yunus ya taya Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a kotun ƙoli
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan takararar Kansila a mazabar Unguwar Tudu dake karamar hukumar Gwarzo Muslim Yunus Abdullahi ya taya Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya samu a kotun ƙoli a shari’un gwamna da aka yanke a ranar jumma,a.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da mai magana da yawun,sa Muhammad Muhammad Zahraddin ya turawa da Jaridar Inda Ranka
Muslim Yunus ya taya Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a kotun ƙoli
Sanarwar ta kara da cewa wannan nasarar da gwamnan jihar Kano ya samu nasara ce ga dimokuraɗiyyar Nigeria.
Abdullahi yace dama shi Sam Sam baiyi tunani rashin nasara a kotin kulin,ba domin kuwa ,ita nasar tana tare damai gaskiya.
“Adan haka Ina miƙa saƙon taya murna ta ga Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf.
“Tabbatar mayar mai da kujerunsa da kotu tayi ya nuna cewa ana bin tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar mu.
Haka zalika ina tabbatarwa da magoya bayan jamiyyar NNPP da al, ummar jihar Kano wajen ci gaba da ayyukan alheri domin koyi jagora Eng Dr Rabiu Musa Kwnkwaso
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa kotun ƙoli ta yanke hukuncin ƙarar da aka shigar a gabanta na zuɓukan gwamnonin da aka yi a shekarar da ta gabata.
