News
Kotu Ta Daure Masu Laifin Fyade Daurin Rai Da Rai A Jihar Jigawa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata Babbar kotun jihar Jigawa mai lamba 6 da ke zamanta a Birnin-Kudu ta samu wani matashi mai suna Habibu Haruna dan shekara 25 da haihuwa da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 14 fyade tare da yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban babbar kotu da laifin janyo yarinyar zuwa dakin matarsa da ke Basirka a karamar hukumar Gwaram.
Alkalin kotun, Mai shari’a Musa Ubable, ya samu wanda ake tuhuma da laifi don haka ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
A lokacin da ake sauraren karar, kotun ta saurari shaidu biyar, sannan kuma lauyan masu gabatar da kara ya gabatar da shaidu uku don tabbatar da karar ba tare da wata shakka ba.
Kotun ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan wanda aka samu da laifin daurin rai da rai bisa sashe na 3 karamin sashe na 2 da na 4 na dokar hana cin zarafin jama’a, dokokin jihar Jigawa mai lamba 2 na shekarar 2021.
