Connect with us

News

Pakistan da Iran sun warware matsalar diplomasiyya da ta gitta tsakaninsu

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

 

Advertisement

Ofishin firaministan rikon ƙwaryar Pakistan, Anwaar-ul-Haq Kakar, ya ce an warware matsalar diplomasiyya da ta gitta tsakanin ƙasar da Iran.

Matakin na zuwa ne bayan da duka ƙasashen biyu suka kai wa juna hare-haren jirage marasa matuƙa da na makamai masu linzami kan sansanonin ‘yan bindiga da ke ƙasashen biyu.

Advertisement

Kotu Ta Daure Masu Laifin Fyade Daurin Rai Da Rai A Jihar Jigawa

Sakamakon abin da ya farun ne kuma ƙasashen biyu suka janye jakadunsu a ƙasashen biyu.

A yanzu ana sa ran jakadun za su koma kan ayyukansu bayan cimma masalahar.

Advertisement

A ranar Alhamis ne Iran ta ce hare-haren da Pakistan ta kai wa ƙasarta sun kashe mutum tara ciki har da ƙananan yara huɗu a kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.

A nata ɓangare tun da farko Pakistan ta ce harin da Iran ta kai ƙasarta a ranar Talata ya kashe ƙananan yara biyu.

Advertisement

To sai dai kawo yanzu Iran ba ta ce komai ba game da wannan batu.

Da safiyar Juma’a ne dai Pakistan ta bayyana aniyarta na yin aiki da Iran don ”magance matsalar” sakamakon kiran hakan daga ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending